Barka da Zuwa Dandamalin Arewa Rising
Arewa Rising shiri ne da aka sadaukar domin wayar da kan jama'a, nuna muhimmanci da karfafa himma wajen habaka tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Arewancin Nigeria a harshen Hausa. Shirin yana da burin baiwa Matasan Arewa kwarin gwiwa a matsayin masu gina ginshikin wannan yanayi na tattalin arziki ta fasaha mai tasowa ta hanyar inganta iliminsu na fasaha da kuma tsara yadda za su zama ainihin ma'aikata a cikin wannan tsarin.
MENENE AREWA RISING
Alfijir na Sabon Fasahar Zamani
Arewa Rising wani shiri ne mai kawo sauyi da aka tsara domin kafa ginshikin haɗa gamayyar yunkurar da fasahar zamani ta hanyar shigar, da karfafa, da kuma baiwa matasan Arewa matsayin zama masu kafa ginshikai, tare da ƙirƙiro da kuma raya tattalin arziki ta fasahar zamani da aka tsara cikin harshen Hausa.
Ta wurin haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki a masana'antu, za mu ba wa Jaruman fasaha, kayan aiki da jagorar fasaha da ake buƙata don samar da ingantaccen tattalin arziki na fasaha da Hausa a matsayin harshen sadarwa na farko wanda a karshe zai sake fasalin yanayin zamantakewa da tattalin arziki na Yankin Arewacin Najeriya.
SABON TSARIN TATTALIN ARZIKI TA FASAHAR ZAMANI A HARSHEN HAUSA
Gano Damammaki
Kafuwar tattalin arziki ta fasahar zamani da za a ƙirƙira a cikin harshen Hausa zai ƙunshi cikakken muhalli na fasahar zamani inda ake haɓaka ayyuka, bayanai, da kayan aiki da kuma samar da su musamman a harshen Hausa.
Wannan tattalin arziki ta fasahar zamanin zai haɗa fasahohin zamani daban-daban kamar su dandamaloli na kasuwanci a yanar gizo, kayan aikin samar da ilimi, kafofin sada zumunta, manhajojin waya, da ayyukan gwamnati, waɗanda aka tsara su don biyan buƙatun masu amfani da harshen Hausa.
RAJISTAR TECH JARUMAI
Kasance Ɗaya Daga Cikin Zaɓaɓɓu
Kuna shirye domin zama majagaba a cikin juyin-juya-halin fasahar sadarwa na Arewacin Najeriya? Shirin Arewa Rising yana gayyatar matasa masu kishi da himma domin su zama na farko a jan ragamar tattalin arziki ta fasahar zamani mai ƙarƙo a cikin harshen Hausa.
Wannan ita ce damar ku don tsara makomarku, haɓaka al'ummarku, kuma ku zama majagaba masu mahimmanci wajen ƙirƙirar shimfidar wuri na fasahar zamani wanda ke magana da harshen mu. Ku rungumi wannan hakki kuma ku kasance tare da mu don kafa tarihi.
Yi rajista yau ka kuma ɗauki matakin farko don zama Tech Jarumi. Tare, mu tashi mu gina gobe mai ma’ana!
A matsayin Tech Jarumi zaka samu:
Tallafin ɗaukar nauyin horar da gwani a fannin fasahar da kuka zaɓa
Datar da ta biya kuɗin samun horonka na kwarewa a yanar gizo
Horo daga ƙwararru a masana'antar
Sanya ku a dandamalin fasahar sadarwa ta zamani don aiwatar da sana'ar ku
Sansanin Koyo na Arewa Rising
Waɗannan shirye-shiryen horaswa a yanar gizo sun ƙunshi ɗimbin fasahohin ƙwarewa masu mahimmanci don haɓaka ƙaƙƙarfan tattalin arziki ta fasahar zamani a harshen Hausa. Kwararru (Tech Jarumai) daga waɗannan sansanonin koyon za su taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban na wannan muhallin, daga haɓaka fasaha da tsaro, zuwa ƙirƙirar abubuwa na fasahar sadarwa da sarrafa kasuwanci.
Ƙirƙirar Gida a yanar gizo
Duration: 6 Weeks
Ƙirƙirar Manhajar Waya
Duration: 6 Weeks
Tallata Haja a Yanar Gizo
Duration: 4 Weeks
Kasuwanci a Yanar Gizo
Duration: 4 Weeks
translations.Content Creation (Graphic Design)
Duration: 6 Weeks
translations.Content Creation (Audio Visuals)
Duration: 6 Weeks
Nazarin Bayanai da Rahottoni
Duration: 4 Weeks
Tsara Cimma Burin Aiki
Duration: 4 Weeks
Tsara Yanayin Samfurori (da Manhajoji)
Duration: 4 Weeks
Al'adantar da Fasahohin Zamani
Duration: 4 Weeks
ZA KU SO KU ƊAUKI NAUYIN BIYAN HORAR DA TECH JARUMI?
La'akari da taimakonku na tallafin ɗaukar nauyin horo a sansanin mu na koyo ba kawai zai ƙarfafa ma jarumai da muhimman ƙwarewar fasahar sadarwa ba amma har da ba da gudummawa sosai ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Tallafin ɗaukar nauyin horo zai ƙunshi biyan kuɗin koyarwa, kuɗin jarrabawa da buƙatun datar intanet ga jarumai - asalin farashin gudanar da horon a yanar gizo a ko ina suke. Farashin kowane Shirin Ba da Horo: N30,000 (Naira Dubu Talatin Kacal)